Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bebeto: Mu Ajiye Duk Wani Son Rai Mu Sa Ci Gaban Wikki A Gaba


A girl plays with a toy gun at a plastics recycling yard in Dhaka, Bangladesh.
A girl plays with a toy gun at a plastics recycling yard in Dhaka, Bangladesh.

Bayan rashin samun damar hayewa zuwa jagaye na gaba a wasan CAF Confederation Cup, da Kungiyar Kwallon kafa ta Wikki Tourist, bata samu ba a bana, an samu cece kuce tsakanin magoya Bayan kungiyar ta Wikki, inda wasu ke ganin laifin mai horas da ‘yan wasanne Moh'd Baba Ganaru, wasu kuwa na ganin laifin na ‘yan wasanne.

A ranar Lahadi data gabata kungiyar kwallon kafa ta Wikki, ta doke RSLAF, ta kasar Sierra Lione, daci daya da babu amman duk da haka bata hayeba Sakamakon Kungiyar RSLAF, ta jefa kwallo biyu da babu a karawarsu ta farko a kasar Sierra Lione.

Sakamakon wannan mahawara Dandalinvoa.com ya sami tattaunawa da wani mamba a Kungiyar magoya Bayan Wikki tourist, mai suna Ibraheem Bebeto, (Mujaddadi) inda yace;

“kungiyar kwallon kafa ta Wikki tourist, tamu ce ta jihar Bauchi, mu ne ya kamata mu nemo hanyar magance matsalar dake damun kungiyar, dan haka ya kamata mu ajiye son ranmu a gefe Mu sa chigaban Kungiyar agabanmu, in bahaka ba kuwa ba zamu haifi da mai ido ba idan har muka duba yadda muka fara wasan kakar bana da Jan kafa, kuma gashi ana samun cecekuce tsakaninmu, wasu suce matsalar daga coach ne wasu suce yadda ake manejin kungiyar ne”.

Ibraheem ya kara da cewa “ko ma waye na yi imanin idan har bamu cire son zuciya ba, wallahi zamu kasa kasau, kuma ya kamata coach kayi adalci duk Wanda yake kokari kaba shi dama yagwada.

ku kuma hukumar dake kula da Kungiyar Management kusa ido kuga abinda yake gudana bisa adalci, magoyabaya muyi goyon bayan gaskiya tunda kullum muna kallon abin dake faruwa”.

Wikki tourist dai a yanzu zata maida hankalintane a gasar firimiya lig na bana, a waccan shekarar kungiyar Wikki ta kare a mataki na ukku a gasar firimiya 2015/2016, a yanzu haka tana mataki na Goma Sha shidda a wasanni 6, da kungiyar ta buga.

A yau kuma zata kara da Kungiyar kwallon kafa ta Shooting Start a filin wasa na tunawa da Sir Abubakar Tafawa Balewa dake Bauchi.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

XS
SM
MD
LG