Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Sanata Ahmed Lawan ya gargadi Gwamnati da kakkausan harshe, yayin da ya ke kashedi ga mahukuntan kasar kan wajibcin hanzarta samar wa matasa ayyukan yi, muddun ana so a kauce wa fuskantar wata sabuwar zanga zanga shigen ‘ENDSARS’ a nan gaba.
Wannan batu ya ja hankalin wasu jiga jigan Jamiyyar APC mai mulki da ma na PDP. Shugaban Majalisar Dattawan ya yi gargadin ne a yayin wani zama don kare kasafin kudin Ma'aikatar Noma a Majalisar Dattawa, inda ya kara da cewa gwamnati ta dauki mataki a aikace wajen shigar da matasa a kasafin na shekara ta 2021, don a dada kwantar da kurar.
Wanan batu ya ja hankalin wani jigo a Jamiyyar APC, Janar Garus Gololo mai Murabus, wanda ya ce ‘Yan Majalisar Dokokin Kasar su ne ya kamata su yi wata doka mai karfi da za ta rage kudaden albashin ‘yan Majalisar da manya manyan ma'aikatan Gwamnati saboda a yi amfani da kudaden wajen yin ayyukan mazabunsu. Gololo ya ce idan sun yi haka shi ne alamun cewa sun taimaka wa Gwamnati wajen magance zaman kashe wando da matasan kasa ke yi a dukkannin kananan hukumomin kasar.
Shi ma daya daga cikin masu magana da yawun Jamiyar PDP, Umar Sani Decat ya ce wannan furuci ba laifi ba ne amma kila yayi kokari ya ba fadar Shugaban kasa shawara amma ba a saurare shi ba, shi ya sa ya fito bainar jama'a ya yi wadannan maganganun. Decat ya ce kwanakin baya ma Sanata Ahmed Lawan ya ce a sauke shugabannin hukumomin tsaro a zauren majalisa, bayan sun yi mahawara akan batun, wanda ya nuna cewa yana so ya wanki kansa ne da majalisar da yake shugabanta.
Shi ma mai nazari kan al'amuran yau da kullum, Kwamrad Isa Tijjani ya ce kiran da shugaban Majalisar Dattawan ya yi ya zo a daidai saboda Shugaban Majalisar Dattawa shi ne na uku a jerin shugabancin kasa, kuma ya san wani abu da kowa bai sani ba. Tijjani ya bada shawarar cewa a hada hannu da Gwamnati a zauna a fitar da hanya da za ta taimaka wa kasa saboda a kauce wa irin barnar da aka yi a zanga zangar ENDSARS.
Matasan Najeriya 10,000 ne suka gudanar da zanga zangar ENDSARS a fadin kasar kwanan nan, inda suka nuna fushinsu a kan cin zarafin mutane da ‘yan sanda ke yi da kuma rashin shugabanci nagari, lamarin da ya ja hankalin Gwamnati.
Ga Madina Dauda da cikakken rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5