Maganin Riga Kafi ya Haifar da Matsala

Yara '

Wani maganin riga kafin kamuwa da fitsarin jini da kumburin ciki da aka baiwa wasu daliban makarantar firamari, a jihar Neja, ya haifar da matsala ga yaran.

Amma jami’an kiwon lafiya a jihar sun ce an sabawa ka’idar shan maganin ne shi yasa aka samu wannan matsalar maganin dai da aka bada shi a karamar hukumar Kontagora shiri ne na hadin gwiwa a tsakanin ma’akatar lafiya ta Najeriya, da ta jihar Neja.

Shugaban karamar hukumar Kontagora, Alhaji Dalha Attahiru, yace sun samu labarin afkuwar wannan lamari, amma darakta, a matakin farko na ma’akatar lafiyar jihar Neja, Dr. Usman Muhammad, yace lamarin da abun damuwa bane illa yaran sun sha maganin ne a daidai lokacin da suke jin yunwa.