Watan azumi wata mai albarka da kowa yake bukatar yasamu rahamar da ke cikin watan, suma mata ‘yan kasuwa ba abarsu a bayaba. Malama Hassana, wadda take sayarda attanfofi tace tayi ragin kayanda take siyarwa a wannan watan da kaso hamsin 50% abun da kuwa yasatayi wannan rangwamen bakomai bane illa tanaso tasamu falalar wannan watan, saboda malamai na wa’azi kancewar yakamata a tausayama masu karamin karfi a wannan watan don neman dacewa da rahamar Allah.
Wanna wa’azin da taji shiyasa ta rage kayanta daga yadda take siyarwa, takuma yi karin bayanin kancewar wannan ragin da tayi babu wata riba da zata samu, illa ma uwar kudin tashige, amma saboda neman albarkar wannan watan tana da yakinin cewar zata maye a wani bangaren.
Malama Hassana, dai bata tsaya a nan ba tana kira ga mata ‘yan uwanta dama maza ‘yankasuwa da suji tsoron Allah su yi kokarin samun falalar da ke cikin wannan watan su rage farashin kayansu, koda wasu masu karamin karfi sun sami rahusa, wanda tahaka ma suma sun samu wata falalar Allah, don su sani fa shi watan ramadana watane da kowa yake kwadayin ya aiwatar da wani aiki na ibada don samun tsira wajen Allah, to yazamana wajibi kowa yayi kokarin ya tausayama al’uma don dacewa da rahamar Allah a wannan wata mai albarka.