Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tilas ne a Hada Karfi da Karfe Kada Abun Yazo ya Addabemu


Bisa ga dukkan alamu matsalar sace mutane domin neman kudin fansa na neman zama matsalar tsaro dake addabar jama’a yanzu a jihar Adamawa, batun da masana ke ganin cewa tashi tsaye ya zama dole.

Na baya bayan nan shine na sace wani basarake wakilin tsaftar masarautar Adamawa, Alhaji Aliyu Aminu Mujeli, da wasu da ba’a san ko su wanene ba suka yi a karshen makon jiya, wanda yanzu haka aka sako shi a jiya alhamis.

Wanan shine karo na hudu a kasa da watani hudu da ake sace fitattun jama’a, a jihar, ko mai hukumomin tsaro a jihar keyi game da wannan batu, DSP, Uthman Abubakar, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, yace wannan wani babban kalubalene da rundunar bata saba fuskantar irin sa ba, masamman ma a jihar Adamawa, amma duk da haka an samar da wani tsari wadda zai dakile wannan harka na sace sace.

Wani mai fashin baki Muhammad Ismail, yace abun yanzu yana nema ya zama sana’a a wurin wasu mutane, yace tilas ne a hada karfi da karfe domin kada abun yazo ya addabemu, ya kara da cewa idan irin waddannan mutanen suka sace mutu basu samu abun da suke bukata ba suna iya kasha shi.

XS
SM
MD
LG