Ya bayyana hakan ne a jiya Laraba yayin liyafar murnar cikar dimokradyiyar Najeriya shekaru 25 ba tare da tsaiko ba, a Abuja.
washington dc —
Shugaban Kasa Bola Tinubu yace zai amince da sabon mafi karancin albashin da gwamnati zata iya biya.
Ya bayyana hakan ne a jiya Laraba yayin liyafar murnar cikar dimokradyiyar Najeriya shekaru 25 ba tare da tsaiko ba, a Abuja.
Shugaban kasar ya yabawa mutanen da suka goya masa baya tsawon shekaru tare da yiwa 'yan Najeriya alkawarin cewar ba zai kaucewa tafarkin mulkin dimokradiyya ba.
Ya kara da cewar, "mafi karancin albashin zai kasance abinda 'yan Najeriya zasu iya biya, zaka iya biya, nima zan iya biya. Zai kasance daidai ruwa daidai tsaki".
Haka kuma shugaban kasar ya sha alwashin rage farashin kayan abinci ta hanyar shawo kan matsalar 'yan bindiga data hana manoma noma gonakinsu.