A lokacin da shugaban Amurka ke neman yadda zai yi da batun Syria sakataren tsaron kasar yace zai sanar da majalisar dokoki duk halin da ake ciki
WASHINGTON DC —
Ahalinda ake ciki kuma, sakataren tsaron Amurka Jim Mattis, yayi alkwari jiya Alhamis, cewa, ma'aikatar tasaron Amurka da ake kira Pentagon, zata "sanarwa" majalisar dokoki duk wani shirin daukar matakin soja akan Syria, kasar da Amurkan take nazarin daukar matakin soja da nufin ladabtarda gwamnatin kasar kan hari da aka kai da makamai masu guba.
Amma abun lura, sakataren na tsaron Amurka bai ambaci batun neman izinin majalisa kamin daukar matakin sojin ba, wadda Amurkan zata auna kan gwamnatin kasar ta sham ko Syria karkashin jagorancin Bashar al-Assad.