Ma'aikatar tace zata shiga jihohin da rigingimun Boko Haram ya daidaita saboda bada tata irin gudummawar.
Zata sake gina gidajen mutanen da rikice-rikicen Boko Haram suka lalata masu muhallansu.
Babban daraktan ma'aikatar Farfasa Muhammad Al-Amin ya bayyana hakan yayin bikin ranar samarda muhalli ta duniya da ake kira World Habitat Daya a turance ranar da kuma Majalisar Dinkin Duniya ta kebe.
An yi bikin ne a sansanin 'yan gudun hijira dake birnin Maiduguri fadar gwamnatin jihar.
Farfasa Al-Amin yace Majalisar Dinkin Duniya ta kebe ranar ce domin tattauna matsalar muhalli da gidaje da kuma inda mutane ke zama. Saboda haka ma'aikatarsa ta ga ya dace su gudanar da taron wannan shekarar a sansanin 'yan gudun hijira wadanda rikici ya rabasu da gidajensu domin tattaunawa akan matsalolin da suke fuskanta da suka jibanci muhalli.
Yace duniya ta damu da irin halin da suka shiga musamman shugaban kasar Najeriya Muhammad Buhari. Da zara sun koma garuruwansu ma'aikatar da kungiyoyi da taimakon mutane zasu sake gina masu gidajensu.
Mutanen dake sansanin sun yi korafe korafe da dama akan matsi da suke fuskanta tare da yoyo da wasu dakunan ke yi idana an yi ruwan sama. Abinci bai wadacesu ba.
Ga rahoton Haruna Dauda Biu
Your browser doesn’t support HTML5