Lura da yadda aka samu tabarbarewar dangantaka tsakanin kafafen labaru masu zaman kansu da ma’aikatar haraji ta kasa DGI sakamakon rufe wasu kafafen ya sa hukumomin dake kula da karbar haraji shirya taron musamman da nufin canza yawu a tsakaninsu da ‘yan jarida ta yadda za a samu fahimta.
Sani Sallau Mamman shine darektan ma’aikatar haraji a shiyyar Yamai ta Kudu. Ya ce a baya sun yi wani aikin rabawa kungiyoyin jarida haraji da suka ga kamar ya yi masu yawa. Lamarin ya kawo cece kuce har ya kawo rashin fahimta. Ya ce dalili ke nan da suka shirya taron su sanar dasu yadda suka raba harajin saboda sun yi aikin ne bisa doka.
Zancen nan da ake ma’aikatan jaridu masu zaman kansu da dama ne ke ci gaba da zaman kashe wando bayan da ma’aikatar haraji ta rufe masu wuraren aiki saboda rashin biyan haraji cikinsu har da jaridar LA GRIFFE wace na zanta da editanta MOUSSA DOUKA
Moussa Douka ya ce babu kungiyar jarida ko wani gidan jarida da ya ce ba zai biya haraji ba amma abun da suka ga dama suka rubutawa kowace jarida. Babu wata jarida da za ta iya biyan kudin sefa miliyan sittin cikin kwana goma.
Kafafen da suka yi kaurin suna wajen sukar lamirin gwamnatin renaissance ne suka fuskanci hushin hukumar ta DGI dalili kenan ake zargin jami’an haraji da taka rawa da bazar gwamnati da nufin huce mata takaici. To amma mai magana da yawun hukumar haraji ya ce tsarin aikinsu ne ya sa suka yi hakan.
Matsalar rashin samun kudaden shigar da suke huskanta ya sa kafafe masu zaman kansu fara tunanin shigar da bukatar a basu wani kaso daga kudaden harajin da ‘yan Niger ke zubawa kafafen gwamnati a karshen kowane wata.
ZABEIROU SOULEY editan jaridar LE TEMPS yace yadda kafofin labaru na gwamnati ke ba jama’a labaru haka su ma su keyi saboda haka su ma a dinga ba su wani kaso.
A saurari rahoton Souley Barma
Your browser doesn’t support HTML5