Al’ummar gari na korafe korafen cewa a yanzu ne ma ake ta rushe gine gine, wani ya ce babu abinda aka fara yi banda rushe rushe, inda suka ce suna murna za’a gyara hanyar Damagarm saboda yadda hanyar ta lallace sosai. Jama’a dai sun ce ba sa tsamanin za’a gama hanyar kan lokaci har a shiryawa zagayowar ranar samun yancin kan kasar.
A cewar jagoran ayyuka na kamfanin Satom Fali Indiga da aka ba su alhakin ayyukan, ya ce lallai suna aikin hanyar sosai kuma za su gama manyan ayyukan kafin 18 ga watan Diamba. Mista Fali ya ce sun samu nassarar cimma kash 60 cikin 100 kawo yanzu.
A shekarar bana an shirya gudanar da bikin zagayowar ranar samun 'yancin kan kasar Niger a Jihar Damagaram, wanda yanzu haka ayyuka sun kankam na gyaran gari da wuraren da za a yi bukukuwan. Tuni dai kamfanoni da yan kwangila suka dukufa wajen ayyukan da dama, kama daga aikin, wajen da za a yi fareti, wajen saukar baki, da gidajen wasanni, zuwa filin jirgin sama da za a mayar da shi na kasa da kasa.
Facebook Forum