Ma'aikatan Kananan Hukumomin Jihar Borno 27 Sun Samu Horo

Gwamnan Borno Kashim Shettima

Wani kamfani da ake kira Adamu Consultancy Limited ya gudanar taron kwanaki ukku wa kananan hukumomi ishirin da bakwai dake jihar Borno domin horas dasu kan yadda zasu gudanar da alamuransu idan sun koma garuruwan da suka fito

Mafi yawan kananan hukumomin sun dawo cikin birnin Maiduguri da zama sakamakon rikicin da kungiyar Boko Haram ta haddasa a jihar da ma wasu jihohin dake arewa maso gabas.

Taron ya tabo batutuwa da dama ciki hadda yadda za'a kula da 'yan gudun hijiran da rikicin Boko Haram ya daidaita tare da yin rugu-rugu da wasu kauyuka. Wasu ma sun samu matsuguni ne a hedkwatar kananan hukumomin. Dole ne a shirya yadda za'a dinga kula dasu har lokacin da zasu samu muhallansu.

Akwai kuma batun kiwon lafiya saboda yawancin asibitoci da wuraren shan magani 'yan Boko Haram sun yi raga-raga dasu. Akwai batun samar masu da ayyukan yi da kuma yadda gwamnatin tarayya zata cika alkawarin tono man fetur a yankin.

Dr Haruna Adamu shugaban kamfanin yayi karin haske akan manufar taron. Yace su ma'aikatan kananan hukumomi ake son a tunatar dasu ayyukan dake gabansu tunda an samu zaman lafiya a yawancin wurare.

Cigaba da samun tsaro hakki ne da ya rataya a wuyan gwamnatin tarayya. Samarda makarantu da asibitoci da ababen more rayuwa suna kan gwamnatin jiha. Amma abu mafi mahimmanci shi ne a tabbatar mutane sun samu aikin yi. Mata suna da aikin yi matasa kuma ba'a barsu kara zube ba. Yakamata a tabbatar manoma sun samu taki isasshe kuma akan lokaci.

Ga rahoton Haruna Dauda da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Ma'aikatan Kananan Hukumomin Jihar Borno 27 Sun Samu Horo - 4' 20"