Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jihohin da Rikicin Boko Haram Ya Daidaita Sun Samu Tallafi Daga Wasu Kasashen Turai


Tawagar Kasashen Tarayyar Turai da suka kawowa arewa masoo gabas tallafin miliyoyin Euro a fadar gwamnan jihar Adamawa
Tawagar Kasashen Tarayyar Turai da suka kawowa arewa masoo gabas tallafin miliyoyin Euro a fadar gwamnan jihar Adamawa

Kungiyar kasashen turai tare da hadin gwiwar ma’aikatar kasafin kudi da tsare-tsare ta kasar Jamus ta samarwa jihohin Adamawa da Borno tallafin yuro miliyan hamsin da hudu da digo biyar .

Da yake kaddamar da shirin a Yola fadar jihar Adamawa, shugaban tawagar Mr, Richard Young yace za a yi anfani da kudin wajen taimakawa ‘yan gudun hijira da al’umomi da ‘yan gudun hijira ke samun mafaka a wurinsu wajen ta hanyar samar masu da muhimman bukatun rayuwa da kuma wadanda ke neman komawa gida don sake gina muhallansu.

Shirin wanda zai dauki tsawon shekaru biyar ana aiwatar da shi zai kunshi sake farfado da ayyukan noma, sana’o’in na dogaro da kai da wanzar da zaman lafiya.

Gwamnan jihar Adamawa Sanata Muhammadu Umaru Jibirilla Bindow a hirarsa da Muryar Amurka ya ce kashi sittin na wadanda zasu anfana daga shirin marayu da mata da aka kashe mazajensu sakamakon rikicin Boko Haram lokacin da yake amsa tambayar makomarsu karkashin shirin tallafin.

Kiyasar hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta nuna kimaniN mutane miliyan biyu da digo biyu rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu.

Ga rahoton Sanusi Adamu da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:16 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG