Ma'aikatan Masakar SOTEX Ta Nijar, Sun Koka Kan Rashin Albashi

Kamfanin Atamfa Na SOTEX A Jamhuriyar Nijar.

Tun bayan da gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta bada dama masu saka jari daga kasashen waje su zo su saka jari a kamfanin SONITEXTILE, wanda daga baya ya koma SOTEX, yanzu haka "yan kasar China sun janye kudadensu, lamarin da ya sa ma'aikatan kamfanin ba su samun albashi.

Yanzu haka ma’aikatan masakar atamfa da ake kira SOTEX a Jamhuriyar Nijar, su na kokawa game da mawuyacin halin da suka tsinci kansu sanadiyar tsayar da ayyukan kamfanin,har suka shafe watannin da dama ba tare da samun albashi ba.

Ma’aikatan sun yi kira ga gwamnati da ta duba wannan lamari, tare da daukar matakin da ya dace.

A yau Litinin, ma’aikatan sun gudanar da wani zaman dirshan a harabar kamfanin na SOTEX, wadannan ma’aikata sun fadawa manema labarai cewa, su na cikin damuwa akan barazanar da kamfanin yake fuskanta na durkushewa, bayan da ‘yan kasar China da su ke da hannun jari mai yawa a kamfanin su ka janye kudadensu.

Kawo yanzu dai tunda ‘yan kasar China suka kwashe kudadensu komai ya tsaya cik a kamfanin na SOTEX, inda kusan shekaru biyu kenan injinan kamfanin ba su aiki.

Ga wakilinmu Sule Mummuni Barma da cikakken rahoton daga Yamai:

Your browser doesn’t support HTML5

Ma'aikatan Kamfanin Atamfa Na SOTEX A Jamhuriyar Nijar, Sun Koka Akan Rashin Albashi