Ma'aikatan sun fara nuna fushinsu ta wajen rufe kofar shiga majalisar da hana mambobin majalisar shiga ciki har sai an biyasu kudadensu.
Hakan na zuwa ne yayin da gwamnar jihar Taraba ke kokarin kai kasafin kudin na shekarar 2023.
Kwamared Bala Ibrahim Yusuf shine Shugaban kungiyar ma’aikatar majalisar dokokin Najeriya reshen jihar Taraba, ya ce sun bi dukkanin matakai domin ganin an biya su hakkokinsu amma abin ya faskara shi yasa suka shiga wannan yajin aikin da sai baba ta gani sai an biyasu hakkokinsu.
A nata bagaren gwamnatin jihar Taraba, ta bakin kwamishinar ma’aikatar yada labarai a jihar, Lois Emmanuel, ta yi kira da ma’aikatan majalisar dokokin jihar Taraba da su yi hakuri gwamnati za ta biya su ba da jima ba.
Masu fashin baki kuma na ganin hakan abin kunya ne ace har tsawon shekaru akwai wasu hakkokin ma'aikatanr ba a biya su ba sai dole sun shiga yajin aikin
A hirar shi da Muryar Amurka, Musa Askira mai fashin baki akan al’amuran yau da kullum, ya ce idan aka duba irin wannan hukucin da ma’aikatan suka dauka akwai fannoni guda biyu, na farko akwai zanga zangar lumana akan hakkin da ya kamata a basu, na biyu idan wannan zanga zanga bata yiwuwu ba za su dauki mataki a wajen yin yajin aiki.
Ya ce idan aka duba kusan abun kunya ne ace shekaru bakwai ita gwamnatin jihar Taraba ta san cewa wadannan hakokokin suna bi ba’a biyasu ba, to ‘yan majalisa kuma suma suna nan sane sun koka wurinsu ba’a biyasu ba to shi yasa yanzu idan suka kulle majalisar babu damar gudanar da harkoki da zai tafi sai an biya su hakkokinsu.
A halin yanzu dai gwamnan jihar Taraba ya kammala duk wasu shirye shirye domin ganin ya kai kasafin kudi na badi a majalisar dokokin jihar sai gashi ma’aikatan majalisar sun shiga yaji aiki.
Saurari cikakken rahoton Lado Salisu Mohammed Garba:
Your browser doesn’t support HTML5