ABUJA, NIGERIA - Ma'aikatan sun zayyana tsohon shugaban na su da wanda ya gurgunta hukumar da danne hakkin ma'aikata.
Tun sanar da nada sabon shugaban hukumar Hussaini Magaji da shugaba Tinubu ya yi a rukunin nade-nade da shugaban hukumomin ma'aikatar kasuwanci; ma'aikatan suka zuba ruwa a kasa suka sha don rabuwa da Barista A.G. Abubakar wanda jikan Firaminista, Sir Abubakar Tafawa Balewa ne.
Shugaban kungiyar ma'aikatan da suka yi shagali a gaban helkwatar hukumar a Abuja, Komred Dokta Ibrahim Kirfi, ya ce yanzu sun samu sabuwar fata ta ingancin aiki "Gaskiya AG. Abubakar bai dau halin marigayi Tafawa Balewa ba don ya dade yana danne hakkin ma'aikata.
Yanzu zamu hada kai da sabon shugaban hukumar don kawo nasarorin da za su taimaki tattalin arzikin Najeriya."
Shi ma ma'ajin kungiyar ma'aikatan, Komred Shamsuddeen Umar Dungus, ya ce tsohon shugaban ya sauya masa wajen aiki da manufar da ba ta dace ba.
Muryar Amurka ta tuntubi AG. Abubakar don jin martaninsa inda ya ce ba zai ce komai ba.
Amma ya yi amannar cewa yana da shaida mai kyau a duk inda ya yi aiki don haka a tuntubi jami'an labarun hukumar.
Rasheed Mahe jami'in labarun hukumar ne da ke cewa ba wani tasiri da gangamin ma'aikatan ya yi.
Hukumar yi wa kamfanonin rajista na daga manyan cibiyoyin da ke samawa gwamnatin Najeriya biliyoyin Naira don haka a ke daukar wanda a ka nada shugaban hukumar ya tafi ma'aikata mai tsoka.
Saurari cikakken rahoto daga Nasiru Adamu El-Hikaya:
Your browser doesn’t support HTML5