Kungiyar ma’aikatan ritayar na wannan korafin ne a yayinda jami’ai a asusun bital malin kasar Nijar ke cewa bincike ya gano dubban ma’aikatan ritaya na bogi da ake fitar da kudade da sunansu daga aljihun gwamnati.
A bisa al’adar tsarin aiki a Nijar ma’aikatan ritaya suna karbar kudaden fansho ne a karshen kowane wata 3. La’akari da yadda abin ke wahalar da tsofafin ma’aikata ya sa gwamnatin kasar a shekarar 2023 bullo da tsarin biyan fansho a karshen kowane wata.
Sai dai a yanzu haka da dama daga cikinsu na fama da rashin samun wadanan kudade, kamar yadda Mahamadou Moussa shugaban kungiyar ma’aikatan ritaya OSYTRAN ya tabbatar mana.
A binciken da ya gudanar a watannin karshen shekarar 2024 ya ce an gano dimbin ma’aikatan ritaya na bogi wadanda a baya ake daukan kudaden fansho da sunansu inji shugaban Baitul Malin kasar na Tesor National Madame Zeinabou Seibou.
Ta ce akwai ma’aikatan ritaya 172 da ba sa raye amma kuma aka ci gaba da daukan kudaden fanshonsu har zuwa lokacin da aka gudanar da bincike.
Haka kuma daga cikin mutane 36,225 da ke rubuce a takardun asusun ma’aikatan ritaya CARENI a watan Agustan 2024 bincike ya yi nunin cewa mutun 32,163 aka tabbatar da halaccinsu kafin daga bisani wasu kusan 1500 su bayyana a tsakanin Satumba da Oktoba. A jumilce ma’aikatan ritaya kimanin 3,113 ne ba sa kan ka’ida a karshen wannan kididdiga.
Kungiyar OSYTRAN wacce ke nuna rashin amincewa da sahihancin aikin binciken ta kudiri aniyar kai batun a gaban mahukunta na koli.
A wani yunkurin magance matsalolin tsofaffin ma’aikata hukumomin kasar suka kafa asusun CARENI mai alhakin kula da kudaden fansho a 2012, to amma rashin gamsuwa da yadda asusun ke kasafin wadanan kudade ya sa hukumar gudanar da baitul malin shirya ayyukan bincike domin kididdige zahirin adadin wadanda suka cancanci samun fansho.
Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:
Your browser doesn’t support HTML5