Yakamata matasa su farka domin su kama sana’a ko da da jari kadan kadan ne domin gujewa dora wa iyaye dawainiya, da zarar matashi ya dan tasa. Matashiya malama Akiba Sani ce ta bayyana haka a yayin da take zantawa da wakiliyar DandalinVOA.
Ta ce da jari kadan matashi zai iya tada jari na sana’ar dogaro da kai muddin bai sa dogon buri ba, inda take cewa lokaci yayi da matasa zasu daina dogara da sai an sami aikin ofis bayan kammala karatun digiri.
Ta kara da cewa bayan ta kammala karatun digiri ta fara aiki a banki amma hakan bai sa tayi kasa a gwiwa ba wajen kama sanaarta ta dogaro da kai, ta ce ta fara koyon aikin kwaliya na mata ne tun tana tsakiyar karatun ta na digiri.
Bayan kammala karatunne ta ga dacewar maida aikin makeup a matsayin wata hanya ta dogaro da kai, sannan a yanzu suna fuskantar matsalar rashin samun kwastomomi kamar da duba da yadda masu harkar kwaliyar amare da sauran matasa kwalliya yawa a cikin al'umma.
Akiba ta ce ana binta har gida domin ta yi wa mutum kwalliya ko kuma ta bi amare gidajensu amma farashinsu ba daya bane.
Your browser doesn’t support HTML5