Lokacin Dogaro Da Kai Domin Huce Takaicin Duniya Ya Yi - Inji Hajiya Saude

Babban kalubalen da ke ci wa harkar hajja ta tuwo a kwarya bai wuce yadda mutane ke kin biyan bashi ba da zarar sun sayi kaya inji malama Sauda Muhammad.

Ta ce ta fara sana'a ne domin ta zamo mai dogaro da kai, ta ce sana'ar maganin kashe kananan bukatu, ta kara da cewa kafin ta fara sana'ar hajja ta kanyi dambun nama , gasara da sauransu .

Sanao'in da ta ke sun taimaka mata wajen yin bukatun gida, kuma ta fara ne ta hanyar sarar kaya daga wajen kawayenta da suke kawo kayan daga daga kasashen waje.

Saude ta bayyana cewa akwai wani lokaci da wata kwastamanta ta rike mata kadi har tsawon shekaru biyar wanda hakan ya sanya jarinta ya karye

Ta kuma ja hankalin matasa da loakci yayi da zasu daina dogaro da abinda samarinsu ke basu, su tsaya kan kafafunsu su zama masu dogaro da kai, don huce wa kansu takaicin zaman duniya.

Your browser doesn’t support HTML5

Lokacin Dogaro Da Kai Domin Huce Takaicin Duniya Ya Yi