Kungiyar kwallon kafar Liverpool ta Ingila ta yi Allah waddai da halayyar wasu magoya bayanta, a lokacin bukin murnar nasarar da ta yi na lashe gasar Premier ta bana.
Liverpool din ta sami tabbacin lashe gasar ne a ranar Alhamis sakamakon galabar da kungiyar Chelsea ta yi akan Manchester City, duk kuwa da cewa akwai sauran wasanni 7 a kammala kakar wasanni.
Murnar nasarar da Liverpool din ta yi na lashe kofi karon farko bayan shekaru 30, ya sa masoyan kungiyar tattaruwa a birnin na Liverpool, inda su ka yi ta wasan wuta da ababen fashewa, duk kuwa da dokokin hana tarukan jama’a da ke akwai a birnin.
Magaji garin birnin na Liverpool ya ce wannan halayya kan iya kawo takun saka tsakanin birnin da kungiyar ta Liverpool.
A daren Juma’a ma an ci gaba da taron murnar da ya hada har da mata da yara kanana, lamarin da ya sa sai da ‘yan sanda su ka shigo domin tarwatsa su.
To sai dai kungiyar ta Liverpool ta wallafa a shafinta na yanar gizo cewa “ba za ta lamincewa wannan hallaya” ta masoyan na ta ba.