Kungiyar kwallon kafar Liverpool ce ta lashe gasar Premier ta Ingila ta bana.
Liverpool din ta lashe gasar ne bayan da a Chelsea ta yi galaba a kan Manchester City a yau da ci 2-1, wanda ya ba da tazarar maki 23 a tsakanin Liverpool din da ke saman tebur da Manchester City da ke bin ta, wanda kuma ba za ta iya kamo ta ba a sauran wasannin da suka rage na gasar.
Wannan ne karo na farko da liverpool din za ta daga kofin na Premier a cikin shekaru 30, tun daga shekarar 1990 da ta lashe kofin.
Kammala wasan na Chelsea da Manchester City ke da wuya, masoyan Liverpool a duk fadin duniya sun soma bukukuwa da tsallen murnar wannan gagarumar nasara a launi ja na kungiyar.
Facebook Forum