Liverpool Ta Yanke Kauna Wajen Sayen Nabil Fekir Daga Lyon

Nabil Fekir

Barcelona, ta ce a shirye take domin kure kungiyar Chelsea, ta hanyar yi mata tayin dan wasan gabanta Ousmane Dembele, mai shekaru 21, da haihuwa domin musayar sa da dan wasan gaban Belgium mai shekaru 27, Eden Hazard, wanda Real Madrid, ke zawarci.

Dan wasan gaba na Crystal Palace, dan kasar Ivory Coast, mai suna Wilfried Zaha, mai shekaru 25, a duniya yana gaba-gaba cikin jerin ‘yan wasan da Marco Silva, yake sha'awar saye zuwa Everton, da dan wasan gaban.

Arsenal da Ingila Danny Welbeck, mai shekaru 27, yana daya daga cikin 'yan wasan da suke so.

Liverpool ta yanke kauna wajen sayen dan wasan tsakiyar daga kungiyar Lyon mai suna, Nabil Fekir, mai shekaru 25, da haihuwa bayan da ta sayi mai tsaron ragar Roma dan kasar Brazil, Alisson.

Manchester City, ta ce zata sayar da dan wasan gabanta Raheem Sterling, nan da watanni 12 in har dan wasan bai sabunta kwantirakinsa a kungiyar ba, dan wasan zai kammala kwantirakinsa ne a shekarar 2020 sai dai kungiyar ta ce bazata yarda ta kai shekarar karshe da wani dan wasa ba tare da ya sabunta zamansa a kungiyar ba.

Danwasan tsakiya na Liverpool, Fabinho, yana kokarin shawo kan abokin wasansa a Monaco Kylian Mbappe, mai shekaru 19 a duniya da ya dawo kungiyar Liverpool. matashin dan wasan dai ya haskaka a gasar cin kofin duniya da ta gabata a kasar Rasha.

Tsohon Kocin kungiyar kwallon Kafa na Arsenal Arsene Wenger, mai shekaru 68 a duniya shine yake kan gaba cikin jerin sunayen wadanda hukumar kwallon kafar Japan ke nema don ya kasance mata Kocin tawagar kasar bayan ya nuna sha'awarsa ta cigaba da hidimar wasanni.

Your browser doesn’t support HTML5

Liverpool Ta Yanke Kauna Wajen Sayen Nabil Fekir Daga Lyon