A ranar lahadi 15/7/2018 aka kammala gasar cin kofin kwallon Kafa ta duniya 2018 wadda ya gudana a can kasar Rasha, Kasar faransa ce ta lashe gasar bayan da ta doke Croatia da ci 4-2.
Dan wasan Croatia Mandzukic, shi ya sha gida (Own Goal) a mintuna 19, daga bisa Pericis, ya rama a minti na 28 inda ake 1-1
Bayan minti 38, dan wasan gaba na faransa Griezmann, ya samu bugun daga kai sai maitsaron gida (penalty) inda ya saka kwallo a zare an tafi hutun rabin lokaci 2-1.
Paul Pgoba, ya saka kwallo ta uku a ragar Croatia, a minti na 59 sai K Mbappe, da ya jefa kwallo ta hudu a minti na 65, Mandzukic ya rama wa Croatia kwallo ta biyu, yayinda ya rage wasu mintoci a tashi haka dai aka tashi a wasan 4-2.
Rabon Faransa da kofin tun shekarar 1998 kimanin shekaru 20 kenan yayin da ta karbi bakuncin gasar.
A wannan gasar an jefa kwallaye 169 a duk wasannin da aka buga, inda aka samu Katin gargadi (Yellow Card) 219, Jan kati (Red Card) 4, Kasar Belgium ita tafi zurara kwallo a gasar inda taci kwallaye 16, sai faransa 14, Ingila 14.
Kaftin din tawagar kasar Ingila Harry Kane, shi yafi zurara kwallaye inda yake da kwallaye 6, an bashi Kyautar (Golden Boot)
An kuma zabi dan wasan Croati Luka Modric a matsayin gwarzon dan wasa a gasar ta bana (Golden Ball) sai Eden Hazard, na Belguim, a matsayi na biyu Griezmann, daga Faransa a matsayi na uku.
Mai tsaron raga na kasar Belgium Thibaud Courtious, shine yafi tsare ci har sau 27 aka bashi Kyautar (Golden Glove)
Dan wasan kasar Faransa Kylian Mbappe shi aka zaba a matsayin matashin dan wasa a gasar kofin duniya 2018 inda yake da shekara 19 da haihuwa.
Facebook Forum