WASHINGTON, DC —
Lashe wasanni har guda 10 da ta yi a jere ya sa a yanzu kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ta Ingila ta hau kan kujerar sama a teburin Firimiya, ta kuma rungumi matsayin da ba ta saba runguma ba: watau kungiyar da ake kyautata zaton zata zamo zakarar wasannin lig-lig na bana a Ingila.
Kuma zai yi wuya a ce za a iya ja mata burki a wannan karshen makon, domin kuwa zata yi tattaki ne zuwa Carrow Road domin gwabzawa da kungiyar Norwich. Idan ba a manta ba a karawar da suka yi sau uku a baya din nan, Liverpool tana zura kwallaye har biyar-biyar a ragar 'yan Norwich.
Ita kuwa kungiyar manchester City, ta yi hasarar maki har biyar a wasanninta biyu na baya, inda ta kara ja da baya a gwagwarmayar neman kambin Firimiya Lig. Yanzu babbar mai hankoron wannan kambi a bayan Liverpool ita ce Chelsea wadda take ta biyu, take kuma baya da maki biyu. Asabar din nan, Chelsea zata gwabza ne da Sunderland wadda ek can kasa.
Yanzu dai sauran wasanni 4 suka rage.