WASHINGTON, DC —
Real Madrid ta doke babbar abokiyar adawarta, FC Barcelona, da ci 2-1 a wasan karshe na gasar cin kofin Sarkin Spain, Copa del Rey.
Wannan shi ne kofin farko da Carlo Ancelotti ya lashe a matsayin manaja na kungiyar Real Madrid.
Gareth Bale, wanda aka yi ta cacar-baki da kushewa a lokacin da Real ta saye shi daga kungiyar Tottenham Spurs ta Ingila, shi ne ya zamo gwarzonta a wannan wasa na yau laraba, inda ya narka kwallo cikin raga ana saura minti biyar a tashi, kwallo da za a jima ana tunawa da shi.
Wannan shi ne karo na uku a jere da ake doke kungiyar FC Barcelona.
Angel Di Maria na Real Madrid ya jefa kwallon farko a minti na 11 da fara wasa, amma ana saura minti 20 a tashi, Marc Bartra ya jefa kwallo da kai ya ramawa 'yan Barca.
Yanzu dai Real Madrid ta lashe kofin na Copa del Rey sau 19 ke nan, yayin da FC Barcelona ta lashe shi sau 26.
An fara wannan gasa tun shekarar 1903.