WASHINGTON, DC —
Wata sabuwar kididdiga ta nuna cewa babu 'yan wasan da suka kai na kungiyar kwallon kafa ta Manchester City samun albashi mafi tsoka a duk duniya, kuma a kowane irin wasa.
Kididdigar da aka fitar yau talata ta nuna cewa idan aka hada albashin 'yan wasan farko na kungiyar Manchester City wuri guda, za a ga kowannensu yana samun kwatankwacin Euro miliyan 5 da dubu 864 a shekarar kwallo ta 2013-2014.
A tsakanin kungiyoyin kwallon kafa na duniya, Real Madrid ita ce ta biyu wajen yawan albashin da 'yan wasanta ke samu, inda in an hada wuri guda za a ga masu buga mata tamaula su na samun kusan Euro miliyan 5 da rabi a shekara, ta kuma FC Barcelona tana ta uku da kimanin Euro miliyan 5 da kusan dubu 400.
Sauran kungiyoyin kwallon kafa dake cikin jerin kungiyoyin wasanni guda 12 da suka fi bayar da albashi mai tsoka a duniya sune Bayern Munich ta Jamus dake lamba ta 7, sai Manchester United a lamba ta 8, sai Chelsea a lamba ta 10, sai kuma Arsenal a lamba ta 11.