“Yanzu haka ina asibitin masu tabun-hankali dake unguwar Yaba a Jihar Legas, bisa dukkan alamu yajin aikin yayi tasiri”, a cewar shugaban kungiyar ma’aikatan asibitocin kula da masu larurar kwakwala dake Yaba a Legas.
Tilas ce ta saka su shiga yajin aikin, domin kwato wa masu jinya da su kansu ma’aikatan hakkokinsu daga shugabanninsu, wadanda suka yi watsi da yarjejoniyoyin da suka cimma da ‘yan kungiyar ma’aikatan a can baya.
Wadannan kungiyoyi dai sun hada da na likitoci, da na ma’aikatan jinya da sauran masu aiki a asibitoci da cibiyoyin lafiya dake fadin tarayyan Najeriya.
Shugaban kungiyar ma’aikatan lafiya reshen asibitin masu fama da tabun hankali, wato Comrade Ozundi Wike ya shaida.
“Yace muna da matsalar kayan aiki. Babu wutar lantarki. Haka kuma ofisoshin da ma’aikatan mu ke zama, basa ganuwa, a cunkushe suke, ta yadda ma’aikaci bashi da sukunin gudanar da ayyukansa.”
Wasu marasa lafiya da ‘yan uwansu suna gani bai dace ma’aikatan lafiya na tafiya yajin aiki ba. Chief Obajide Obadino ya shaida wa Muryar Amurka cewa ya kai ‘yar uwarsa ne asibitin, amma kuma bukatar su na ganin likita ko samun magani bai samu ba.
Your browser doesn’t support HTML5