Likitocin sun kira wannan taro ne domin fadakar da sauran ma’aikatan asibiti dangane da cutar ta Ebola, saboda sune suke fara karo da masu cutar, lamarin da ka iya kaisu ga daukar cutar.
Amma likitocin sun koka akan cewa gwamnati bata yi tanadin wadatattun kayan kariya ba daga wannan cuta.
Daya daga cikin likitocin yace “bamu yarda ba, ko kadan na cewa an dauki hanyar kare mu, mu ma’aikatan asibiti, daga wannan cuta, saboda haka muke rokon gwamnati tayi abunda ya kamata.
Yanzu haka dai an kwashe makonni shida, likitoci a duk fadin tarayyar Najeriya suna cikin yajin aikin sai baba ta gani, biyo bayan rashin jituwa da suka samu da gwamnatin Tarayya.