Kungiyar likitocin Najeriya ta sanar da sabon matakin tsunduma zanga-zanga a gewayen ma’aikatun lafiya a fadin Najeriya don tilastawa hukumomi biyawa likitocin bukata.
Zanga-zangar da kungiyar likitocin ta kira da ta lumana zata fara ne daga ranar Laraba 9 ga watan Agusta 2023.
Wannan ya biyo bayan matakin da gwamnatin Najeriya ta yi niyar dauka na cewa baza ta biya albashi ga ma’aikatan da ba sa zuwa aiki ba wato wadanda suka auka yajin aiki kamar yadda kungiyar likitocin ta yi.
Mataimakin sakataren kungiyar likitoci masu neman kwarewa NARD Dr. Nura Umar ya ce tsaida biyan albashin ma’aikatan da gwanatin ta ce zata yi tamkar barazana ce, kuma hakan ba zai hana su gwagwarmaya da jajircewa wajen neman hakkin su ba.
Ku Duba Wannan Ma Mun Shiga Yajin Aiki Ne Don 'Yan Najeriya Su Amfana - NARDDr. Nura Umar, ya kara da cewa likitocin za su yi zanga-zangar ne don su nuna fushin su tare da yin Allah wadai da gwanatin da bata damu da al'ummar ta ba, inda ya ce idan aka cigaba a haka, za a wayi gari babu likitoci da za su duba marasa lafiya a asibitocin kasar.
Kamar dai yadda gwamnatin Najeriyar ta yi a gargadin aukawa zanga-zangar ‘yan kwadago na daukar matakan hana zanga-zangar ta hanyar cigaba da tattaunawa, har yanzu irin matsayar gwamnatin kenan kan matakan ma’aikatan.
Idan za’a iya tunawa likitocin sun sanar tsunduma yajin aiki na sai baba ya gani ne tun a ranar 26 ga watan jiya.
Saurari rahoton a sauti:
Your browser doesn’t support HTML5