Liberia ta nemi taimakon Amurka akan binciken mutuwar Greaves

Shugabar Liberia Ellen Sirleaf

Gwamnatin Liberia ta nemi Amurka ta taimaka mata, kan binciken da ake yi game da mutuwar Harry Greaves, tsohon shugaban kamfanin matatar man kasar, wanda aka tsinci gawarsa a gabar wani ruwa dake Monrovia.

A ranar 31 ga watan Janairu aka tsinci gawar Greaves wacce har ta fara rubewa.

Mr Greaves ya kasance dan asalin kasar Liberia ne, ya na kuma shiga harkokin siyasa, yakan kuma soki manufofin gwamnatin shugaba Ellen Johnson Sirleaf

A baya, wani kwararre a fannin binciken kwakwaf kan mamata a nan Amurka, ya yi ikirarin cewa ruwa ne ya ci Greaves, sai dai sakamakon wannan bincike bai gamsar da ‘yan kasar ta Liberia ba.

A halin da ake ciki yanzu, ministan yada labaran kasar ta Liberia, Eugene Nagbe, ya ce gwamnatin kasar ta nemi Amurka ta taimaka mata, domin itama ta damu ta ga an gano musabbabin mutuwar Harry Greaves.