Legas: Jami’an Tsaro Sun Musunta Rahotan Bama Bamai a Agege

Gwamnan jihar Legas Mr Akinwunmi Ambode

Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta musunta rahotannin da ke cewa an gano bama bamai kirar gida a garin Agege.

A karshen wani taron tsaro a jihar Legas, da gwamnan jihar Mr Akinwunmi Ambode ya jagoranta, kwamishinan ‘yan sandan jihar yace babu wani kanshin gaskiya game da rahotannin da ake bazawa na cewa an gano wasu bama bamai kirar gida a garin Agege.

Cikin wannan makon ne dai aka fitar da rahotan na cewa an gano makaman, wanda hakan ya sanya mazauna garin firgita, wasu kuwa sun kwashe nasu ya nasu domin ficewa daga yankin.

Mallam Mohammadu Sani Agege, mazaunin garin ne kuma ya shaidawa wakilin Muryar Amurka dake Legas, Babangida Jibrin, cewa da farkon fitowar rahotan hankalinsu ya tashi matuka, amma daga baya bayan da jami’an tsaro su kayi bayani hankula sun kwanta.

Jihar Legas dai na ‘daya daga jihohin da a can baya jami’an tsaro suka sha kama mutane da ake kyautata zaton ‘yan kungiyar Boko Haram ne, lamarin da ya kai ga mayar da su jihar Borno, domin gudanar da bincike da hukunta su. Hakan yasa gwamnan jihar Legas yayi kira ga mazauna birnn Legas da su rika taimakawa jami’an tsaro da bayanai kan duk wani wanda basu amince da zirga-zirgarsa ba.

Domin karin bayani saurari cikakken rahotan Babangida Jibrin daga Legas.

Your browser doesn’t support HTML5

Legas: Jami’an Tsaro Sun Musunta Rahotan Bama Bamai a Agege - 2'10"