Lauyoyin jami’iyar adawa ta NDP ta uwargidan tsohon shugaba Rawlings ce suna shirin shigar da kara a kotu a birnin Accra yau Alhamis, a kan hukuncin da hukumar zabe ta yanke na hana uwargidan tsohon shugaba Rawalings Nana Konadu Agyemang (AJIMAN) Rawlings bata cancanci ta tsaya takara a zaben shugaban kasa da Ghana zata yi ranar Bakwai ga wata Disamba.
WASHINGTON, DC —
Babban sakataren jami’iyar ta NDP Mohammed Frimpong yace a kwai hannun yan siyasa a dakatarwar da aka yiwa yar takarar tasu, uwargidan tsohon shugaban kasa saboda tana zama barazana ga shugaba mai ci yanzu John Dramani Mahama, na jami’iyar NDC mai mulki, wanda ake ganin zai fuskanci babban kalubale a gwabzawar da zasu yi da dan takarar babban jami’iyar adawa ta NPP Nana Addo Dankwa Akufo Addo.
Frimpong ya karanto dokar zaben Ghana ta CI 94 yana kalubalantar hukumar zaben cewa dokar zaben ta bukaci hukumar zaben ta sanar da jami’iya duk wasu kura kurai dake cikin takardun shiga takara don ta gyara.