Bayan da Majalisar Wakilai ta kada kuri'ar amincewa da safiyar shekaran jiya Laraba, sai aka gabatar ma Majalisar Dattawa, inda aka amince da gagarumin rinjaye, wato dukkannin 'yan Majalisar 39 sun amince. Yanzu kudurin dokar na jiran Shugaba Pierre Bkurunziza.
Ko ma bayan kada kuri'ar da kasar ta yi ta ficewa daga ICC, dole sai gwamnatin kasar ta rubuta takarda ma Sakatare-Janar na MDD don bayyana niyyarta ta ficewa, kuma ficewar za ta fara aiki ne kawai bayan shekara daya da karbar wasikar.
"Zuwa yau dai ba mu karbi wata takarda mai nuna niyyarsu ba," a cewar mai magana da yawun MDD Stephane Dujarric. "Shakka babu, muddan mu ka samu irin wannan takardar, to zai zama abin takaici."
Ficewar Burundi daga kasashen da su ka amince da ICC, za ta zama ta farko a tarihin kotun ta ICC.