Lauyoyi A Kano Sun Yi Gangami A Kan Shan Miyagun Kwayoyi

Lauyoyi

A karshen mako ne kungiyar Lauyoyi ta Najeriya ta gudanar da wani gangami da tattaki zuwa fadar Sarkin Kano domin ankarar da Jama'a game da illolin ta'ammali da miyagun kwayoyi da abubuwan sa maye.

Lauyoyin sun yi wannan gangami ne a wani bangare na bukukuwa da tarukan makon Lauyoyi da kungiyar kan gudanar shekara-shekara.

Gangamin lauyoyin a kan ababen sa maye na zuwa ne mako guda bayan da gwamnati tarayyar Najeriya ta haramta shigar da magungunan dake dauke da sanadarin codeine cikin kasar musamman ma magani tari.

Atoni Janar kuma kwamishinan shari’a na jihar Kano Barr Ibrahim Muktar, yace gwamnatin jihar Kano zata kafa hukumar dakile ta’ammali da miyagun kwayoyi da kayayyakin sanya maye.

Alhaji Hamza Umar dake zama kwamandan reshen jihar Kano na hukumar NDLEA mai yaki da tafauci da miyagun kwayoyi na kasa, ya bayyana gamsuwa a kan yadda lauyoyin suka shiga cikin al’amuran yaki da ababen sanya maye a tsakanin al’umma.

Hakan dai na zuwa ne a daidai lokacin da aka dade ana zargin lauyoyi da kokarin bada kariya ga dillalan safarar miyagun kwayoyi a kotunan Najeriya daban daban.

Your browser doesn’t support HTML5

KANO LAWYERS ON DRUGS