Lauyan Amurka na musamman Jack Smith, wanda ya jagoranci shari’ar gwamnatin tarayya da ake yi wa Donald Trump, bisa zargin kokarin murde kayen da ya sha a zaben shekara ta 2020, da kuma karkatar da wasu bayanan sirri, ya yi murabus, yayin da zababben shugaban kasar na jam’iyyar Republican ke shirin komawa fadar White House.
Smith ya yi murabus daga ma’aikatar shari’a a ranar Juma’a, kamar yadda wata kotu ta shigar a ranar Assabar ga alkalin gunduma na Amurka, Aileen Cannon, inda ta bukaci ta dage umarnin kotu da ta bayar na hana fitar da rahotonsa na karshe.
Sanarwar murabus din Smith ta zo ne a cikin bayanin da aka rubuta a cikin takardar, wanda ya ce lauyan na musamman ya kammala aikinsa, ya mika rahotonsa na sirri na karshe a ranar 7 ga watan Janairu, kuma ya "janye" daga Ma'aikatar Shari'a a ranar 10 ga watan na Janairu.
Smith, tsohon mai gabatar da kara kan laifukan yaki, ya gabatar da biyu daga cikin tuhumar laifuka hudu da Trump ya fuskanta bayan barin ofis, to amma kuma suka tsaya cik bayan da wani alkalin da Trump ya nada a Florida ya kori tuhuma daya, yayin da kuma Kotun Kolin Amurka, da ke da alkalai uku da Trump ya nada, ta yanke hukuncin cewa tsofaffin shugabannin kasa suna da rigar kariya daga fuskantar tuhuma kan wasu ayyukan gwamnati.
Dukan tuhumomin ba wanda ya kai ga zaman shari'a.
Bayan Trump ya doke mataimakiyar shugaban kasa ta jam'iyyar Democrat Kamala Harris a zaben ranar 5 ga watan Nuwamba, Smith ya janye shari'o'in biyu, yana mai nuni da dadaddiyar dokar ma'aikatar shari'a kan gurfanar da shugabannin kasa da ke kan mulki.
A yayin da ya ke neman kotuna da su yi watsi da tuhume-tuhumen, tawagar Smith ta kare sahihancin kararrakin da suka gabatar, amma suka yi nuni da cewa komawar Trump a fadar White House ne kawai ya sa ba za su iya nasara ba.
Murabus din na Smith wata alama ce ta rugujewar tuhume-tuhumen da ake yi wa Trump, wadanda ke iya ƙarewa ba tare da wani sakamako na shari'a ba ga shugaban kasar mai jiran gado, suka kuma haifar da koma baya da ya taimaka wajen dawowar martabar siyasarsa.