Lauya Alex Van Ya Amince Da Shatawa Hukumar FBI Karya

Lauya Alex Van Zwaan yayinda yake isa kotun inda ya amsa laifinsa

Lauya Alex Van der Zwaan ya gurfana akotun Washington DC inda ya amsa laifin yiwa hukumar FBI karya a binciken zargin katsalandan da Rasha ta yi a zaben shugaban kasar Amurka na shekarar 2016

Wani lauyan dake zaune a birnin London ya amsa laifin yin karya ga masu binciken Amurka a kan alakarsa da Rick Gates, tsohon ma'aikacin kamfen na Shugaba Donald Trump, a wani bangare na binciken dake kara fadada kan katsalandar da Rasha tayi a zaben Amurka na shekarar 2016.


Ofishin mai bincike na musamman Robert Muller shi ne ya bayyanar da zargin da ake yiwa lauyan Alex Van der Zwaan da safiyar jiya Talata, kana daga bisani ya amince da aikata laifin a gaban wata kotun Washington. Van der Zwaan, sirikin hamshakin attajirin nan ne na kasar Rasha German Khan kuma yayi aiki a wani sanannen kamfanin lauyoyi a New York mai suna Skadden, Arps, Slate, Meagher & Flom, kafin kamfanin ya sanar da cewa ya kore shi a bara.


Ofishin Mueller mai bincike na musamman, yayi zargin cewa, yayin da Van der Zwaan yake aiki da Skadden, yayi karya cewa, sun yi maganar karshe da Gates a tsakiyar watan Agustan shekarar 2016. A shekarar 2012, ma'aikatar shari'a ta Ukraine ta dauki hayar wannan kamfanin lauyoyi domin ya zana masa rahoto kan hujjojin gurfanar da tsohuwar firayim Ministar Ukraine Yulia Tymoshenko, a gaban kotu, wadda aka ce an same ta da laifin sata da yin amfani da ikonta ta hanyoyin da ba su dace ba, aka daureta, amma kuma daga baya aka wanke ta daga aikata wadannan laifuka.

Masu gabatar da kara sun yi zargin cewa Van der Zwaan yayi karya, a lokacin da yace bai san dalilin da yasa ba a mikawa ofishin mai bincike Mueller wani sakon email tsakaninsa da wani wanda ba a bayyana sunansa ba, a cikin watan Satumbar 2016, alhali kuwa ya goge sakon ne.