Kotun Da Ke Sauraron Kararrakin Zaben Shugaban Kasa A Najeriya Na Shirin Yanke Hukunci

Kotun Karar Sakamakon Zaben Najeriya

Yau Laraba Kotun sauraron karar zaben Shugaban kasa za ta yanke hukumci bayan kwanaki dari da rantsar da Bola Ahmed Tinubu a matsayin Shugaban kasa.

Matakin kotun ya zo ne bayan kammala sauraron jawaban karshe na sassan da ke cikin karar a watan jiya.

Yanke hukuncin zai zo ne mako biyu gabanin cikar wa'adin kwana 180 na ka'idar sauraro da yanke hukuncin bisa doka kuma ya shafi jam'iyyar PDP, Leba da APM da ke bukatar kotun ta soke ayyana Bola Tinubu da hukumar zabe ta yi a matsayin wanda ya lashe zaben.

Dan takarar babbar jam'iyyar adawa PDP Atiku Abubakar da mai bi ma sa baya Peter Obi na Leba na zayyana zaben a matsayin wanda aka nuna murdiya da kin amfani ko bayyana ainihin sakamakon na'urar tattarawa da aika sakamako.

Obi-and-Atiku-2.gif

A hirar shi da Muryar Amurka, Lauya mai zaman kan sa a Abuja Barista Mainasara Kogo Umar ya ce koma yaya shari'ar ta kaya duk wanda bai gamsu ba na da damar garzayawa kotun koli.

A nashi bayanin, Kakakin shugaba Tinubu Ajuri Ngelale ya ce shugaban ya na da kwarin guiwar samun nasara a sakamkon shari’ar.

Shi kuma daya daga manyan jami’an kamfen na PDP Alhaji Yusuf Dingyadi ya ce sun gabatar da duk hujjojin da su ka dace don neman kawar da Tinubu daga fadar Aso Rock.

A na sa bangaren kakakin kamfen din jam’iyyar Leba Yunusa Tanko ya yi zargin katsalandan a shari’ar amma ya ce hankalin su a kwance ya ke bisa hujjojin da su ka bayar.

Za a gabatar da zaman yanke hukuncin kai tsaye ta gidajen talabijin don biyan muradun jama'ar kasa.

Saurari rahoton a sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

Kotun Karar Sakamakon Zaben Shugaban Najeriya Za Ta Yanke Hukunci A Larabar Nan