Akwai Rashin Tsaro Tsakanin Nijer Da Burkina Faso

Aika aikar ‘yan bindiga akan hanyar Burkina Faso zuwa jamhuriyar Nijer ta fara jefa matafiya cikin halin zullumi ganin yadda wannan al’amari ke kara tsananta a tsakanin wadannan kasashe 2 makwabtan juna.

A wata hira da wakilin Muryar Amurka a Yamai Souley Moumouni Barma, wani dan jarida Abdoul Razak Ibrahima da ya bi hanyar Ouagadougou zuwa birnin Yamai, yace lokaci ya yi da jami’an tsaro za su fara raka motoci daga wannan kasa zuwa waccan don kare matafiya daga irin wadannan hare hare.

Abdoul Razak ya kara da cewa motar hayar da ta kai shi Ougadougou ta fada tarkon ‘yan bindiga a yayinda ta ke kan hanyar komawa birnin yamai inda aka cinna mata wuta kuma aka kashe fasinjoji. Haka shi ma lokacin da yake kan hanyar komawa gida ya auna arziki domin sauran kiris da motarsu ta taka nakiya.

Rashin musanyar bayanai tsakanin jami’an tsaron Nijer da na Burkina Faso na taimakawa ma ‘yan ta’adda wajen tafka ta’asa a kauyukan da ke tsakanin kasashen 2 saboda haka ya zama wajibi hukumomi su dubi wannan lamari.

A karshe ya ce lokaci ya yi da jami’an tsaro za su fara raka motoci akan hanyar dake tsakanin jamhuriyar Nijer da Burkina Faso domin kare jama’a da dukiyoyinsu.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

Lalacewar Tsaro Tsakanin Nijer Da Burkina Faso