Har yanzu dai matafiya da fasinjoji na nuna takaicinsu dangane da tafiyar hawainiyar da ake fuskanta wajen gyaran manyan titunan da suka hada manyan biranen kasar daban-daban.
Hanyoyin da lamarin ya fi muni sune wadanda suka tashi daga kudancin Najeriya zuwa Arewacin kasar, da kuma na yammacin kasar zuwa Arewacin Najeriya. Hanyar da ta tashi daga Legas zuwa Makwa da Makera a jihar Neja, har ma zuwa birnin gwari a jihar Kaduna na ‘daya daga cikin hanyoyin da ke ciwa matafiya tuwa a kwarya.
Duk da yake tuni aka gyara gadar da ta karye a kwanakin baya tsakanin Makwa da kuma Jaba, bayan ziyarar da mataimakin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo ya kai. wata gadar da har yanzu ake ci gaba da fuskantar matsala akanta itace ta wadda ke kan hanyar Makwa zuwa Makera dake garin Bokane, wadda karyewar gadar yasa manyan motoci yin dogon zagaye.
Wasu direbobin da Muryar Amurka ta zanta da su sun nuna damuwarsu game da yadda suke kwashe kwanaki suna zagaye kafin zuwa inda zasu.
Yanzu haka dai Najeriya na da hanyoyi masu tsawon kilomita dubu 35 a karkashin gwamnatin tarayya, kuma duk da cewa an kashe musu zunzurun kudi har fiye da Naira Tiriliyan daya da rabi daga shekarar 1999 ta 2015. Irin wadannan hanyoyi basa biyuwa cikin sauki ga masu ababen hawa.
Domin karin bayani saurari cikakken rahotan Babangida Jibrin.
Your browser doesn’t support HTML5