Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jamiyyar APC Mai Mulkin Nigeria Ta Mayar Da Martani.


 Janar Muhammadu Buhari a Kano, Janairu 20, 2015.
Janar Muhammadu Buhari a Kano, Janairu 20, 2015.

Biyo bayan hirar da tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya Alhaji Atiku Abubakar yayi a sashen Hausa na Muryar Amurka yasa wani jigo a jamiyyar mayar masa da martani

Daya daga cikin jiga-jigan jamiyyar APC a jihar Gombe, Injiniya Sa’ad Abubakar yace magangannun da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar yayi game da Shugaba Muhammadu Buhari da gwamnatinsa basu dace ba.

Injiniya Saad yana magana ne da wakilin Sashen Hausa na Muryar Amurka na jihohin Bauchi da Gombe, wato Abdulwahab Mohammed.

Injiniya Sa’ad yace sailin da Atiku Abubakar ya fahinci cewa jam’iyyar su karkashin shugaba Muhammadu Buhari ta fara samun matsala to kamata yayi ya nemi ganawa da shugaba Buhari amma ba ya shiga kafofin watsa labarai yana sukan jamiyyar ba.

Injiniya Saad ya bayyana tsohon mataimakin shugaban kasar a matsayin mutumin da ya goge a harkar siyasa.

Ga Abdulwahab Mohammed da ci gaban wannan tattaunawar.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:09 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG