LAKURAWA: Kalubalen Tsaro A Yankin Sahel Na Afirka

Bincike ya nuna cewa asali Lakurawa mayaka ne da ke fada da zaluncin da suke ganin ana yi wa Buzaye da Fulani, wadanda suka yi suna kan dukiyar dabbobi da ke yawon kiwo a cikin dazuka, kafin daga baya su rikede su koma 'yan ta'adda.

Lakurawa ko Lakura-Fulbe a harshen Fulatanci, ko La Kura da Larabci, wani jinsin mutane ne daga wasu kasashe daban-daban na Sahel, daga ciki akwai Nijar, Mali da Burkina Faso da sauransu.

Bincike ya nuna cewa asali Lakurawa mayaka ne da ke fada da zaluncin da suke ganin ana yi wa Buzaye da Fulani, wadanda suka yi suna kan dukiyar dabbobi da ke yawon kiwo a cikin dazuka, kafin daga baya su rikede su koma 'yan ta'adda.

A yayin da gwamnatocin Najeriya da sauran kasashen yankin Sahel suke bayyana azama wajen yaki da 'yan ta'addan Lakurawa, masana na ganin cewa fahimtar mayakan da kuma hadin gwiwar kasashe, su ne manyan gimshikan samun nasara a wannan yakin.

A kan haka ne cibiyar wanzar da zaman lafiya ta jami’ar Usmanu Danfodiyo ta Sokoto, ta shirya wani babban taron tattaunawa na masana da masu ruwa da tsaki daga ciki da wajen Najeriya, domin fadada masaniya kan Lakurawa da ayukansu.

Taron Tattaunawa Da Fadakarwa Na Yanar Gizo Kan Lakurawa

Labaran Bello Tangaza, jami'i ne a cibiyar bunkasa zaman lafiya ta Afirka maso yamma. Ya ce a fafutukar samar da kariya daga masu yi wa Fulani da Buzaye sata, sun kafa kungiyar ta mayakan da suka kira da suna "Lakurawa" suka saya musu makamai domin su kare dukiyar su.

Bincike ya nuna cewa Lakurawa sun sami nasarar janyo hankalin mutane ta hanyar ikirarin da suke yi na bin addinin Musulunci, abin da ya sa suka sami karbuwa har suka dauki mutane masu yi musu aiki, suka yi auratayya tsakaninsu da mutanen yankunan da suka fara sauka a wuraren su a lokacin zuwan su na farko.

Dokta Murtala Ahmad Rufa'i na Jami'ar Usmanu Danfodiyo da ke Sakkwato mai bibiyar lamuran tsaro a Afirka ta yamma, yace wannan matsala ta sha gaban yakin kasa daya tilo, don haka dole ne sai kasashen Najeriya, NIjar, Mali, Benin da Burkina Faso sun hada kai da karfi kafin su iya kawar da ita.

A cewar masana, daya daga cikin barazanar su, shi ne yadda suke amfani da kayan fasahar zamani wajen tafiyar da ayukkan su na ta'addanci, kamar amfani da kananan jiragen saman leken asiri marasa matuka wajen samun bayanai, da kuma yadda suke hadewa da barayin daji suna aiki tare.

Masana na ganin muddin ana son samun galaba wajen fada da wadannan 'yan ta'ddar dole sai jama'a da gwamnatoci sun fahimci ko su waye Lakurawa, da yadda ayukkansu suke.

Wannan ne babban dalilin shirya taron na yanar gizo, wanda ya hada hancin masana, manyan jami'an gwamnatoci da masu ruwa da tsaki, a cewar daraktan cibiyar kula da wanzar da zaman lafiya ta Jami'ar Usmanu Danfodiyo ta Sokoto, Farfesa Mukhtar Umar Bunza.

Bunza ya ce hakan zai ankarar da hukumomi da jama'a a kan wannan barazanar.

Yanzu haka dai mazauna yankunan da wadannan 'yan ta'addar ke ziyarta, sun ce suna fuskantar babbar barazana

Sai dai kuma mahukunta sun ce suna kan fama wajen yakar wadannan mutanen kamar yadda rundunar sojin Najeriya ta bayyana kokarin da take yi a kan wannan matsalar.

Ga cikakken rahoton Muhammad Nasir:

Your browser doesn’t support HTML5

LAKURAWA: Kalubalen Tsaro A Yankin Sahel Na Afirka