Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Damuwa Kan Bacewar Masu Adawa Da Gwamnati A Kenya


Masu Zanga-zangar Adawa A Kenya Ta Kin Karin Kudin Haraji Da Tsadar Kayan Masarufi A Kasar
Masu Zanga-zangar Adawa A Kenya Ta Kin Karin Kudin Haraji Da Tsadar Kayan Masarufi A Kasar

An zargi dakarun tsaron kasar wadda ke yankin gabashin Afirka da kamawa da tsare mutane da dama ba bisa ka'ida ba, tun bayan zanga-zangar adawa da gwamnati da matasa suka yi a watannin Yuni da Yuli.

Kungiyoyin kare hakkin bil adama da lauyoyi da ’yan siyasa a kasar Kenya sun bayyana matukar damuwa kan yadda aka sake sabunta yawaitar sace-sacen mutane inda ake auna masu sukar lamirin gwamnati.

An shirya wata ‘yar karamar zanga-zanga a garin Embu da ke arewa maso gabashin kasar, inda wani matashi mai shekaru 24, Billy Mwangi, ya bace a karshen makon da ya gabata.

An zargi dakarun tsaron kasar da ke yankin gabashin Afirka da kamawa da tsare mutane da dama ba bisa ka'ida ba, tun bayan zanga-zangar adawa da gwamnati da matasa suka yi a watannin Yuni da Yuli.

William Ruto, Shugaban Kasar Kenya
William Ruto, Shugaban Kasar Kenya

'Yan sanda sun musanta hannu a lamarin, amma masu fafutuka sun saka ayar tambaya kan dalilin da ya sa ba’a ganin suna gudanar da bincike kan bacewar mutanen.

Kungiyar Lauyoyin Kenya ta ce musantawar da babban sufeto-janar na 'yan sanda ya yi a baya-bayan nan bai isa ba, tana mai kira da ya dauki tsauraran matakai a kan masu sace mutanen ko kuma ya yi murabus.

Kungiyar kare hakkin bil adama ta Human Rights Watch ta fada a farkon wannan shekara cewa, binciken ta ya nuna yatsa kan wata runduna ta musamman da aka kafa daga hukumomin tsaro da dama.

Tsohon mataimakin shugaban kasar Rigathi Gachagua, wanda aka cire bayan takaddama da Ruto a kan zanga-zangar, shi ma a jiya Juma'a ya yi zargin cewa wata rundunar sirri ce ke da hannu wajen bacewar mutanen.

Rigathi Gachagua, Tsohon Mataimakin Shugaban Kenya
Rigathi Gachagua, Tsohon Mataimakin Shugaban Kenya

Gachagua ya fada a wani taron manema labarai cewa “kashe su ba shine mafita ba. ...Wannan ita ce gwamnati ta farko a tarihin kasar nan da ke kai wa yara hari don muzguna musu.”

Hukumar kare hakkin bil'adama ta Kenya (KNCHR) ta fada a ranar Alhamis cewa wasu mutane dauke da makamai da ba’a tantance ko su waye ba, sun yi awon gaba da mutane 82 tun daga watan Yuni, inda har yanzu mutane 29 ba’a san inda suke ba.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG