Al'ummomin da ke zaune kan iyakokin Najeriya da Jamhuriyar Nijar sun ce ba su taba ganin wani jami’in soji farara fata ba a yankunansu, duk da yake suna fama da ayyukkan 'yan ta'addar Lakurawa.
Wannan na zuwa ne lokacin da ake ci gaba da mayar da martani kan kalaman da Shugaban Gwamnatin Soji a Nijar ya yi game da sansanin sojin Faransa a Najeriya.
Yankunan da ke kan iyakokin kasashen Najeriya da Jamhuriyar Nijar da yawan su suna fama da matsalolin rashin tsaro, musamman yanzu da aka samu bullar 'yan ta'addan Lakurawa duk da yake mahukunta na kokarin shawo kan matsalar a yankunan.
Wannan da wasu matsalolin tsaro ba su rasa nasaba da yadda wasu ke zargin akwai alamun cewa sojojin kasar waje sun samu gurbin shigowa Najeriya da sunan za su taimaka a yaki da 'yan ta'addar, kamar yadda wasu suka ce an samar da sansanin sojojin Faransa a yankin Borno, kuma kwatsam sai ga Shugaban Gwamnatin Sojin Jamhuriyar Nijar ya kara jaddada wanna zancen.
Sai dai al'ummomi da ke zaune kan iyakokin kasashen biyu watakila su ne kan iya kasancewa na farko da za su iya ganin wadannan sojoijn idan sun shigo Najeriya kuma kan haka ne na ziyarci wasu yankunan da ke iyakar kasashen biyu ta jihar Sakkwato da ke arewa maso yammacin Najeriya domin jin ta bakin mazauna wuraren. Wadanda suka shaida min cewa babu wani sojan wata kasa daga ketare.
Har ma wadanda ke yawon kasuwanci daga Nijar suna shigowa Najeriya sun ce ba su taba ganin wani abu mai kama da sojioji fararen fata ba tun daga cikin Nijar har Najeriya.
Sai dai a cewar wasu matsalar 'yan ta'addar Lakurawa har yanzu ba ta kau ba.
Shugabannin al'ummomin sun ce dangantakar mutanen kasashen biyu kyakkyawa ce kuma wannan batun ba zai sauya ta ba domin 'yan uwan juna ne.
Duk da wadannan kalaman da martani da wasu mutane ke mayar wa, mahukuntan Najeriya na ci gaba da kokarin fatattakar 'yan ta'addan Lakurawan, kamar yadda na shaida girke jami'an soji a yankin Gudu inda nan ne ake jin cewa cibiyar Lakurawan take a Najeriya, da kuma yadda sojin sama da na kasa ke kai musu hare-hare a iyakokin kasar.
Saurari cikakken rahoton Muhammad Nasir daga Sakkwato:
Dandalin Mu Tattauna