Lagos Zata Rage Cunkoson Mutane Da Ababen Hawa

Ministan Makamashi, Aiyuka da Samarda Gidaje

Daga cikin mahimman aiyukan da za’a gudanar sun hada da gina wani hanya mai tsawon kilomita 61, da zai kasance da layukan motoci 5, na zuwa 5,na dawowa

Wasu Al’umomin jihohin Najeriya, na bayyana fargaban su game da karbo bashin miliyoyin daloli da jihohi suke yi duk da matsalar rashin kudi da ake fuskanta.

Daga cikin mahimman aiyukan da za’a gudanar da wadannan kudade sun hada da gina wani hanya mai tsawon kilomita 61, da zai kasance da layukan motoci 5, na zuwa 5, na dawowa wanda zai tashi daga birnin Lagos zuwa Badagry, ya hade da jamhuriyar Benin, da kuma kilomita 27, na jirgin kasa da zai ratsa birnin Lagos, domin rage cunkoson jama’a, da ababen hawa.

Ministan aiyuka kuma tsohon Gwamna a jihar Lagos Babatunde Raji Fashola, wanda ya tabbatar da amincewar bada wannan bashi yace tun kafin zamani da yake Gwamna ne yakamata ace an bada wadannan kudade a wani yarjejeniya da Gwamnati jihar dana tarayya suka amince akai amma banbanci siyasa tsakanin gwamantocin Lagos da suka shude da kuma Gwamnatin tarayyar Najeriya da ta shude ya hana abada wadannan kudade.

Gwamnati de ta dage cewa bashin bai tattare da wani ruwan kudi mai yawa dan haka baa bun damuwa bane ga al’umar jihar kamar yadda ‘yan adawa ke kokawa.

Shugaban hukumar samar da ruwan sha a jihar Lagos, Architect Kabir Ahmed, wanda ma’aikatar shi ke daya daga cikin wadanda zasu amfana da bashi da za’a karbo, yace cikin ikon Allah, an gabatar da shirye shirye da tsare tsare daban daban akan yadda za’a samu nasara kuma za’a inganta samarda ruwa mai kyau da kuma hana gurbata ruwa dake cikin kasa mun dauki matakai na bada izini ga mutane masu sani wadanda ke da fasahar yadda za’ayi a fido ruwan da kuma yadda za’a yada shi ga jama’a.

Wani mazaunin Lagos Abdul lateef Olajire, yace yana goyon bayan karbo wannan bashi idan de za’a yi amfani da shi wajen gudanar da aiyukan raya kasa amma bawai a karkatar dashi zuwa aljuhun wasu ba kamar yadda yanzu muke ganin wasu sun karkatar da kudaden da aka samar domin siyan makamai domin yaki da kungiyar Boko Haram, muna goyon bayan Gwamnati idan dai za’a gudanar da aiyuka da wadannan kudade.

Your browser doesn’t support HTML5

Lagos Zata Rage Cunkoson Mutane Da Ababen Hawa - 3'40"