Ladabi Rigar Mutunci - Inji Musan Waka

Musa Iliyasu wanda aka fi sani da Musan waka, matashi kuma dalibi da ke waka da zummar isar da sakonni ga ‘yan uwansa matasa domin a nusar da su wasu dabi’unsu na zamani da basu da amfani.

Ya ce yana isar da sakonni kamar na yadda matasa ke yawan yin chat suke kuma bata lokacinsu maimako su yi ayyukan amfanar da rayuwarsu.

Musan waka ya ce a wakar da yayi ta soyayya tana nuna yadda ake soyayya a yanzu, yadda mata ke yi wa samari karya da ma yadda matasa ke zama masu zauna gari banza suna hirarrakin da basu dace ba kan wayar salula maimako su maida hankali wajen karatu ko sana’ar dogoro da kai

Musan waka ya ce Kalubalen da suke fuskanta bai wuce na kayan aiki ba mussaman ma ga kananan mawaka kamar sa domin idan suna da bukatar rera waka sai sun tafi studio sun biya kudi da sauransu.

Ya kara da cewa wasu lokutan ma idan aka gayyace su sha’ani na biki shima sai sun yi hayar kayan aiki kamar su abin Magana na speaker da sauran abubuwan da zasu bada amsa amo.

Ya ce akwai wakar bayyana ladabin da ya kamata a rika lura da su kamar cin abinci a tsaye, gaisuwa, Magana da sauransu.

Ku biyo mu domin jin cikakkiyar hirar mu da Musan Waka