Bisa al’ada, bayan an kammala azumin watan ramadana, ana gudanar da bukukuwan Sallah, inda ake ziyartar ‘yan uwa da abokan arziki a wurare daban daban da bada kyaututtuka ga juna.
Samari da ‘yan mata kan mikawa juna kyauta kama daga sutura, kudi kayan kwalliya da sauran abubuwa makamantan su, har ma wasu da dama kan rabu da ‘yan matan su sakamakon rashin abin da zasu ba su a matsayin na shan ruwa ko goron salla.
Irin wadannan samari kan boye da sunan ibada, domin kauracewa ‘yan mata a cewar wasu daga cikin wadanda dandalinvoa ya sami zantawa da su. Sun kara da cewa da zarar azumi ya karato samari da dama kan yi batan dabo amma da zarar an kammala azumi sai su fara neman shiri.
Me zaku ce game da matasa masu irin waddan dabi’a?. ku cigaba da kasancewa da dandalinvoa domin jin yadda wannan hira ta kasance.
Facebook Forum