WASHINGTON D.C —
Kamar da wasa wani sabon fim din Indiya da aka nuna satin da ya wuce wanda yak e nuna yadda mata ke fama da rashin isassun makewayi a kasar Indiya ya sami karbuwa fiye da tsammani a kasar China.
Wannan fim mai suna AKSHAY Kumar –starrer ‘Toilet – Ek Prem Katha, labarin soyayya ne, da ya mamaye kasuwar fin-finan India a China, kawo yanzu fim din ya sami kudi sama da dalar Amurka miliyan $1.3, a fara nuna fim dinne a watan Agustan shekarar data gabata a kasar India.
Masu fashin baki sun bayyana cewa fim din yayi kasuwa da farin jini a kasar China a sakamakon wasu bayanai da kuma harkokin da aka hada a cikin sa da kamfanin hada fina finai na kasar China ba yayi.
Facebook Forum