JUNAIRU: Labarin da yafi daukan hankulanku a watan Junairun wannan shekara shine na Wani bincike da wasu shehunan malamai suka gudanar a Nigeria, wanda ya nuna cewa akwai Masallatai da yawa dake kasar wadanda basa kallon al-Qibla da kyau. Shiekh Abubakar Ibrahim babban Malami ne a Kaduna.
“Bincike da muka yi a garin Kaduna, sai muka ga cewa da yawa Masallatai, ba’a gina su suna fuskantar inda Allah Yace a fuskanta ba, wanda shine matsayin kibla, ma’ana Masjid Haram wanda ya kewaye Ka’aba a nan Macca”.
FEBRAIRU: Ran 2 ga watan Fabrairu ne aka tashi da labarin Wasu 'yan bindiga sun bude wuta a kan motar daya daga cikin mashahuran malaman Sunni na Najeriya, Sheikh Muhammad Awwal Albani Zaria, suka kashe shi tare da matarsa da wani dansa. Sheikh Abbas Isa Lauya babban Malami ne a Najeriya.
“Wannan labari mai muni, mai ban firgici, kwarai da gaske yazo mana a cikin dare, misalin karfe goma”.
MARIS: Ran 3 ga watan Maris ne ‘yan Sanda a Gombe suka kame wani mutum mai lalata da diyarsa. DSP Faje Attajiri shine kakakin hukumar ‘yan sandan Jihar Gombe.
“Mun samu bayanin cewa wannan mutum, yana lalata da ‘yarshi, kuma shima yayi mana bayani cewa yana wannan abun, don yana so ya samu kudi”.
AFRILU: A watan Afrilu ne wani sojan Najeriya wanda muka sakaye sunanshi ya bayyanawa Muryar Amurka cewa akwai sojojin Najeriya a Boko Haram.
“Sojojin da suke bullowa ta daji, wadanda an gudu an barsu, wasu da yawa suna bullowa suna ajje bindigansu suna wucewa gidansu”.
A wannan wata ne ‘yan bindiga suka sace dalibai mata sama da 200 daga makarantarsu ta sakandare dake Chibok a Jihar Borno.
“A can an tara su a karkashin dorawa, da mun fara bi, muka ga kaman baza mu iya mu tunkaresu ba, muka koma baya”.
MAYU: Labarin da yafi jan hankula watan Mayu shine na ikirari da mafarauta a Jihar Borno sukayi ran 16, na cewa suna neman izinin gwamnati domin shiga dajin Sambisa domin ceto daliban Chibok.
“Mu daji bai bamu tsoro, duk gari da kaga an kafa shi, maharbi ne ya kafa shi. Kuma a da can, ba dan sanda, ba soja, ba dan doka, ‘ya’yanmu ne aka kama”.
YUNI: Idan muka je watan Yuni labarin da yafi daukan hankali shine ne kalaman Sheikh Dahiru Bauchi dake cewa gwamnatin Najeriya tayi abun kunya, dangane da badakalar Sabon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu.
“Wannan abun kunya ne. Meyasa aka nada Sarki a Gombe ba’a yi komai ba? Don kawai jam’iyyarsa ba daya ba da mutanen Kano? Abubuwa da ake boyewa zasu bayyana a fili kennan”.
YULI: Sai watan Yuli lokacinda Sojoji a Najeriya suka kashe ‘ya’yan Sheikh Ibrahim El-Zakzaky.
“Wannan abunda ya faru, ya nuna mana a sarari cewa muma yanzu an maishe mu Gaza, abunda akewa Falasdinawa ake mana”.
AGUSTA: Abunda akewa Falasdinawa ake mana. Sheikh El Zakzaky kennan. A watan Agusta aka kammala taron kasa wanda ya share watanni. Wannan labarin shine yafi daukan hankula wannan wata.
“Sanata Sa’idu Umar Kumo, wakili ne a taron cikin wakilan gwamnatin Jonathan “akwai wani kundun tsarin mulki daban da aka rubuta, wanda ba’a yi maganarsa, shine aka saka a White Envlope. Shi babu wanda yake maganarsa, saboda haka babu ruwanmu da wannan.”
SATUMBA: Babban labarin watan Satumba shine na kashe mayakin Boko Haram Abubakar Shekau da rahotanni suka ce sojojin Najeriya sun aiwatar.
“Jama’a na ta binciken ganin tabbacin wannan zahirin na cewa ko wannan da jami’an sojan Najeriya suka bada hotonsa a matsayin Shekau, lallai cewa shine aka kashe shi, don a shekarar da ta gabata an bayyana wani da aka ce shine Abubakar Shekau wanda jami’an sojan Najeriya suka ce sun kashe shi”.
OKTOBA: A watan Octoba ne wani mutum ya fito yace shine Abubakar Shekau, kuma yana nan da ranshi da lafiyarshi. Mike Omeri kakakin gwamnatin Najeriya ne.
“Ai abunda gwamnati ta fada shine, bayan wannan Shekau wani zai sake fitowa, domin haka ne akayi a kwanakin baya”.
NUWAMBA: A karshen watan Nuwamba ne ‘yan bindiga suka fasa boma-bomai da kuma harbe-harbe a Babban Masallacin Juma’a na gidan Sarki dake Kano. Ga wani wanda ya ga abunda ya faru.
“A dai-dai lokacin da liman yace “Allahu Akhbar”, ya tada kabbarar Sallah, a dai-dai lokacin ne aka ji fashewar wani abu a wajen Masallaci, to Amma wannan bai sa liman ya tsayar da Sallah ba, aka cigaba da Sallah to daga baya sai Bom din ya tashi a cikin Masallaci, sai harbe-harbe suka biyo baya”.
DISAMBA: A farkon watan Disamba ne aka kama wani jirgi dauke da kayan yaki a tashar jirgin Saman Mallam Aminu Kano dake Jihar Kano. Mahmoud Ibrahim Kwari shine wakilin Muryar Amurka a Kano.
“Hukumomin tsaro a Tashar Jiragen Sama ta Mallam Aminu Kano sun kama wani jirgi da aka ce yana makare da makamai, baya ga makaman kuma, ance akwai kananan jirage guda uku masu saukar ungulu, ance akwai bindigogi da alburusai da sauran abubuwa.”
Sannan ran 10 ga wata ne shahararren dan wasan Hausa Rabilu Musa dan Ibro ya rasu a birnin Kano. Nura Abubakar masoyin Ibro ne.
“Gaskiya rashi da aka yi na Rabilu Musa wato Ibro ba karamin rashi bane a Kannywood gaba daya”.
Labaran da suka fi daukan hankula ke nan a wanann shekara wadanda muka kawo muku. Zaben shugaban kasa a shekara ta 2015 na daga cikin batutuwa da duniya take zubawa idanu ta ga yadda zata kaya tsakanin Shugaba Jonathan, da Janar Muhammadu Buhari mai ritaya. Sashen Hausa na Muryar Amurka zai cigaba da bin diddigin muhimman batutuwan dake wakana a yammacin Afirka da ma sauran duniya. Ku cigaba da kasancewa da mu kamar yadda muke tare da ku kodayaushe.
Ga rahotannin labaran.
Your browser doesn’t support HTML5