Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kiran A Inganta Matakan Tsaro


Wasu Jami'an Tsaro Na Sintiri
Wasu Jami'an Tsaro Na Sintiri

A cigaba da bitar abubuwan da su ka auku a shekara mai shudewa, wani mai tsokaci kan al'amuran tsaro mai suna Dr. Bawa Wase ya yi kiran da a dau kwararan matakai don inganta tsaro na Nijeriya.

Mai sharhi kan al’amuran tsaro Dr. Bawa Abdullahi Wase y ace ya kamata jami’an gwamnati su san cewa shigo da makamai wai don a baiwa wasu miyagun da ake amfani da su wajen tursasa ma wani bangare na kasa ba ya haifar ma kasa da mai ido samsam. Ya ce yin mu’amala da miyagu wajen gudanar da harkokin gwamnati bai haifar da da mai ido a tarihi.

Ya ce ya kamata duk wata gwamnati ta yi la’akari da abin da ya ce Linda Thomas-Greenfield, Mataimakiyar Sakataren Harkokin Afirka na Amurka (Assistant Secretary of Africa Affairs) ta fada a Abuja ranar Alhamis 5 ga watan 9, 2014 a lokacin bude taro tsakanin Amurka da Nijeriya kan hanyoyin ciyar da kasa gaba, inda ya ce ta ce “Lokacin girman kai da gwamnati ta Nijeriya ta ke yi ko kuma yaudarar mutanenta da sunan Boko Haram ya wuce. “ Ya ce ta ce idan ko aka ki jin shawararta to “za a wayi gari fa – wannan abun ba wai kadai zai kare a yanzu ba, ‘ya’yan da su ke a Nijeriya a nan gaba ba su da madogara, su wadanda su ke rike da mulkin Allah kadai ya san yadda za su kubuta” Ya Linda ta ce wajibi ne gwamnati ta nada wadanda su ka cancanta a mukaman da su ka jibanci tsaro, ba kawai a nada mutun saboda dalilai na siyasa ba.

Ya ce ya kuma kamata gwamnati ta sama wa matasa ayyukan yi saboda a duk inda ka ga ana tashin hankali a duniya akasari matasa ne marasa ayyukan yi. Ya ce ba wai kowa sai ya shiga ofis ya na aiki ba. Muddun aka wadata wuta da ruwa hakan zai taimaka matasa su yi sana’o’i irinsu wanki da guga da noma da dai sauransu. Ya ce ya kuma kamata a yi cikakken bincike da kuma daukar mataki kan rahoton Dr. Steven Davis wanda ya alakanta Ali Madu Sherriff da Ehijirika da Boko Haram.

Dr. Wase ya kuma yi nuni da batun wani katafaren jirgin saman da ya sauka a filin jirgin saman Kano dauke da wasu kayakin da aka yi ta takaddama akai. Ya ce an yi ta jayayya kan ko waye mai jirgin kafin aka yi ta samun bayanan alakar jirgin da kasashen Faransa da kuma Rasha. Ya kuma ce zargin zuwan Ali Madu Sheriff wurin jirgin abun dubawa ne sosai.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG