Shugaban hukumar kwastan Kanar Hamid Ali mai ritaya, ya ce matakin kwastam na yin rijistar motocin ba an ‘dauke shi bane da nufin gallazawa talaka, sai dai neman masu motocin da basu biya kudaden harajinsu ba kawai.
Kamar yadda rahotanni ke cewa jami’an hukumar kwastam za su tsare hanya suna bincikar motocin da ba a biyawa haraji ba sun kwace motocin. A cewar shugaban hukumar kwastam, wannan batu ba haka yake ba, jami’an kwastam zasu dakon masu sabunta takardun motocinsu a cibiyoyin daban-daban da ake da su a fadin ‘kasar, idan aka samu motar da ake bi haraji za a tilasta mata biya.
Tuni dai ‘yan Najeriya ke Allah wa dai da matakin hukumar Kwastam, inda suke ganin zai takurawa masu ‘karamin ‘karfi.
A cewar tsohon mataimakin shugaban hukumar Kwastam, Alhaji Ibrahim Musa Gongwazo, matakin hukumar yana bisa doka kuma zai taimaka wajen ‘karawa hukumar kudaden shiga.
Domin karin bayani.