A wata hira da sashen Hausa ya yi da shugaban karamar hukumar Madagali, Alhaji Mohammed Yusuf, lokacin wata zirayar da masu ruwa da tsaki na karamar hukumar suka kai sansanin soja a Madagali don jinjinawa da baiwa dakarun kwarin gwiwa.
Gwamnan jihar Adamawa, Muhammadu Umaru Jibrilla Bindo, wanda ya ce “yabon gwani ya zamo dole,” ya bukaci mazauna yankin su ja hakulan ‘yan uwansu dake zaman hijira da su koma gidajensu da yake yanzu zaman lafiya ya samu a yankin.
Kwamandan rundunar ta 143 dake da sansani a Madagali, Kanal Chidi Nlemadin, ya shaidawa tawagar cewa rufe kasuwar garin da rundunar ta yi, ta wucin gadi ce don kaucewa hare-haren kunar bakin wake da ake kaiwa watannin baya kan kasuwar. Ya ce rundunar ba zata jira har sai ‘yan ta’addar Boko Haram sun kai hari kafin su maida martini ba, ya ce suna bin su cikin daji suna fatattakarsu.
Wakilin Muryar Amurka, Sanusi Adamu, ya ziyarci yankin ya ce wata babbar matsala da yankin ke fama da ita, ita ce ta rashin hanyoyin sadarwa ta wayoyin salula, sakamakon lalata tasoshin sada sakonni da ‘yan ta’addar Boko Haram suka yi shekaru uku da suka wuce.
Domin karin bayani saurari rahotan Sanusi Adamu.
Facebook Forum